Sojin Saman Nijeriya Sun Yi Nasarar Lalata Makaman Boko Haram Wanda a Dajin Sambisa

167

Rundunar Sojin Saman Nijeriya tayi nasarar lalata makaman kungiyar Boko Haram wanda yake Gujeri, cikin dajin Sambisa na Jihar Borno.

Rundunar ta ce dakarunta ne na Operation Lafiya Dole ne suka kai harin.

Jami’in hulda da Jama’a na rundunar Ibikunle Daramola shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa wanda aka rabawa manema labarai a Abuja.

Ibikunle Daramola ya ce jami’an rundunarta sun kai harin cikin daren Talata, bayan sun sami rahoton sirri kan cewa yan kungiyar ta Boko Haram zasu kai hari zuwa kyauyen na Gujeri.

Kazalika ya ce rundunar tasu ta kai harin ne kan wasu Bishiyoyi, inda yan kungiyar ta Boko Haram suke ajiye makaman su da kuma kayan Abincin su.

Haka kuma ya ce jami’ansu zasu cigaba da kaiwa hare-hare a yankunan Arewa Maso Gabas domin ganin sun kori mayakan na Boko Haram gaba daya. 

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 + 7 =