Shugaba Buhari Ya Taya Gwamnatin Jamhuriyar Nijar Da Jama’ar Kasar Jimami Bisa Harin Ta’addanci

111

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zanta da Shugaban Jamhuriyar Nijar, Muhammadu Isufu ta wayar tarho domin jajanta masa da gwamnatinsa da jama’ar jamhuriyar Nijar bisa harin ta’addanci na ranar 9 ga watan Janairu a kasar.

Wasu wadanda ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai hari kan sansanin soji a garin Chinagodrar dake jamhuriyar Nijar, akan iyakar kasar da Mali, inda suka kashe sojoji da dama.

Kakakin Shugaba Buhari, Mallam Garba Shehu, a cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja, yace Shugaban kasa Buhari ya bayyana jimami tare da yin ta’aziyya ga iyalai da abokan mamatan.

Da yake Allah wa dai ga harin ‘yan ta’addan, Shugaban kasa ya tabbatarwa da takwaransa na jamhuriyar Nijar cewa Najeriya zata cigaba da aiki kafada da kafada da kasarsa da sauran abokan huldar kasa da kasa wajen shawo kan ta’addanci.

Shugaban kasa sai ya tabbatarwa da wadanda suka kitsa harin da wadanda suke daukar nauyinsu cewa basu cancanci zaman lafiya da jin dadi ba, inda ya jaddada cewa kasar Najeriya tana goyon bayan kawayenta wajen tabbatar da cewa an hukunta su.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × three =