Hukumar Jiragen Kasa ta Karyata Labarin Hari Kan Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja

101

Manajin Darakta na hukumar jiragen kasa ta kasa, Mista Fidet Okhiria, ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya jajircewar hukumar wajen tsaron lafiyar fasinjoji akan hanyar jirgin kasa ta Kaduna zuwa Abuja.

Fidet Okhiria ya shaidawa manema labarai cewa abinda hukumar ta fi mayar da hankali akai shine tabbatar da sufurin dukkan fasinjoji zuwa inda suka nufa lami lafiya.

Daga nan sai ya karyata zargin da wasu jaridu ke yi cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wani jirgin kasa dauke da fasinjoji daga Kaduna zuwa Abuja.

Jaridun sun bayar da rahoton cewa wasu mutane dauke da makamai wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne a yau da safe sun kai hari kan jirgin kasan wanda ya nufi Abuja.

Rahoton yayi zargin cewa jirgin, wanda ya bar tashar jiragen kasa ta Rigasa a Kaduna da misalin karfe 10 na safe, an kai masa hari a wani waje kusa da garin Katari, mai nisan kimanin kilomita 70 zuwa Abuja.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 + twelve =