Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Kulle Haramtattun Shagunan Dura Iskar Gas Na Gefen Titi Guda 87

47

Hukumar kare muhalli ta jihar Kaduna tace ta kulle haramtattun shagunan dura iskar Gas na gefen titi guda 87 a jihar, biyo bayan fashewar tukunyar gas da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 5.

Janar Manaja na hukumar, Jibrin Lawan, ya bayyana haka yayinda ake share wajen da tukunyar ta fashe, lamarin da ya auku ranar Asabar a unguwar Sabon Tasha, cikin yankin karamar hukumar Chikun.

A cewar Jibrin Lawal, rufe shagunan yana kan umarnin Gwamna Nasir el-Rufa’I, biyo bayan fashewar da tayi ajalin mutane 5 tare da raunata wasu mutane 4.

Yace anyi aikin rufe shagunan lokaci guda a garuruwa 3 na jihar Kaduna, inda aka rufe shaguna 54 a Kaduna da 25 a Zaria tare da guda 8 a Kafanchan.

Shugaban hukumar yace dura iskar gas aiki ne mai hadari wanda bai kamata ake gudanar da shi a kusa da gidajen mutane ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

6 + thirteen =