Gwamnati Tarayya Ta Karbi Sabbin Jiragen Yaki Guda Biyu

170

Gwamnatin tarayya ta ce tana daf da kawo sabbin Jiragen yaki guda 2 domin yaki da yan kungiyar Boko Haram da kuma Yan Bindiga.

Shugaban Sojojin Sama na kasa Air Marshal Sadique Abubakar shine ya bayyana haka ciki wata tattaunawarsa da manema labarai a fadar shugaban kasa, bayan ganawar da shugaban kasa yayi da shugabannin tsaro na kasa a fadarsa dake Abuja.

Shugaban kasa Muhammad Buhari, shine ne ya shirya ganawar da shugabannin tsaron a fadarsa dake Abuja.

Air Marshal Sadique Abubakar, ya ce za’a kawo sabbin jiragen ne tare da sauran kayan da Rundunar Sojin sama suke bukata, domin ninka kokarinsu a yakin da sukeyi da yan ta’adda.

Haka kuma ya ce kasar Nijeriya tanayin hadin gwiwa da sauran kasashen da suke makotaka da ita domin yakar mambobin kungiyar Boko Haram.

Kazalika, ya bukaci yan Nijeriya, dasu bada gudunmawarsu domin magance matsalolin tsaro da suke damun kasar nan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eleven − 9 =