Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta bayar da gudunmawar kayan abinci ga kungiyoyin mata da gidajen gyaran da’a da gidajen marayu da sauran kungiyoyin marasa karfi a jihar Gombe.
Uwargidan gwamnan jihar Gombe, Hajiyar Asama’u Yahaya ce ta raba kayan abincin a wani taro a Gombe.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya bayar da rahoton cewa kayan abincin da aka raba sun hada da buhunhuna 1000 na shinkafa da katan 600 na taliya sai jarkar man girki 300.
Da take jawabi wajen taron, Hajiya Asama’u Yahaya tace an bayar da gudunmawar ne da nufin tallafawa rayuwar wadanda suka amfana.
A nasa jawabin, mai taimakawa uwargidan shugaban kasa kan yada labarai, Mallam Abdullahi Aliyu, yace an yanke shawarar rabon kayan abincin ne domin taimakawa mabukata.
Shugaban kungiyar nakasassu, Alhaji Umar Goro, ya godewa uwargidan shugaban kasar bisa karamcin da tayi, tare da kiran ta kara kokari.