Yansanda a Jihar Nasarawa Sun Kame Wani Mai-Gari Bisa Zargin Taimakawa Masu Garkuwa Da Mutane

48

Rundunar yansandan jihar Nasarawa ta kame Alhaji Dalhatu Abubakar, mai garin Mangoro Goma a kauyen Tunga cikin yankin karamar hukumar Nasarawa, bisa zargin taimakawa masu garkuwa da mutane.

Kwamishinan yansanda, Bola Longe, shine ya bayyana haka a Lafiya yayinda yake gabatar da maigarin da sauran wadanda ake zargi su 80 ga manema labarai.

A cewar Bola Longe, yansanda sun kame mai garin biyo bayan samun bayanan sirri bisa samunsa da hannu a garkuwa da mutane akan titin Loko zuwa Toto a Nasarawa.

Yace daga ranar 22 ga watan Oktoba zuwa yanzu, rundunar ta kame mutane 46 wadanda ake zargin masu garkuwa da mutanene, da kuma yan kungiyar asiri su 35. Yansanda sun kuma kwace bindigogi 9 da harsasai 34 da keke napep 3 da Babura 2 da motoci 3, a wannan lokacin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × 1 =