Yan Boko Haram Sun Mamaye Wani Kauye A Chibok

85

Wasu wadanda ake kyautata zaton yan kungiyar Boko Haram ne ana zargin sun kashe wasu mutane 5 fararen hula tare da sace wasu da dama, yayin da suka mamayi wani kauye a kusa da garin Chibok a yankin karamar hukumar Chibok ta jihar Borno, a jajiberin kirsimeti.

Rahotanni sunce lamarin ya auku ne jiya da misalin karfe 6 na yammaci a kauyen Korogelem, mai nisan kilomita 10 daga garin Chibok.

Majiyoyi sunce maharan sun rushe gidaje da dama bayan sun yashe gidajen tare da kwashe kayan abinci.

A cewar majiyar ‘yan kato da gora, maharan sun rinjayi sojoji kafin su rike kauyen na tsawon awanni, bayan fararen hula sun arce zuwa dazuka domin tsira da rayukansu.

Wani mazaunin garin, mai suna Musa Bitrus, ya shaidawa manema labarai cewa maharan sun gudu da kayan abincin da aka shirya domin bukukuwan kirsimeti.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 + thirteen =