Hukumar DSS ta sake cafke Omoyele Sowore

55

Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS ta sake kama Omoyele Sowore, wanda ya shirya zanga-zangar juyin juya hali, tare da wanda ake tuhumarsu tare, Olawale Bakare.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya bayar da rahoton cewa Sowore da Bakare sunyi turjiyar sake kama su da jami’an za suyi, jim kadan bayan mai shari’a Ijeoma Ojukwu ta dage sauraron karan har zuwa ranakun 11 da 12 da 13 na watan Fabrairun 2020.

Mai Shari’a Ojukwu a jiya Alhamis ta bayar da umarni ga hukumar DSS ta saki Sowore da Bakare cikin awanni 24, bayan ya cika dukkan sharuddan belinsa.

Mai shari’ar wacce ta bayar da umarnin, ta kuma ce DSS ta biya tarar kudi Naira Dubu 100 saboda jinkirin da tayi wajen bayar da karin hujjoji ga lauyan wadanda ake kara.

Hukumar ta DSS a jiya Alhamis ta bi umarnin kotun inda ta saki wadanda ake karar tare da biyan tarar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × three =