Gwamnatin Kano na sa ran yiwa yara miliyan 3 da Dubu 800 rigakafin sankarau

33

Gwamnatin Jihar Kano tana sa ran yiwa yara akalla miliyan 3 da Dubu 800, ‘yan shekara 1 zuwa 7, rigakafin sankarau, a kananan hukumomi 44 dake fadin jihar.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar da Mallam Abba Anwar, kakakin gwamna Abdullahi Ganduje ya fitar a Kano.

A cewar Abba Anwar, Gwamna Ganduje ya bayyana haka yayinda yake kaddamar da gangamin rigakafin a kauyen Danlasan da ke yankin karamar hukumar Warawa ta jihar.

Gwamna Ganduje sai yayi kira ga jama’ar jihar su shiga aikin, tare da tabbatar da cewa sun gabatar da ‘ya’yansu wajen rigakafin domin cigaban kiwon lafiyar al’umma.

Gwamnan sai ya tunawa mutane wasu cututtukan dake addabar al’umma.

Yace gwamnatinsa ta gyara tare da samar da kayan aiki ga cibiyoyin lafiya kimanin 300 dake fadin jihar, a wani bangare na sabunta yunkurin samar da ingatattacen kiwon lafiya a jihar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two + fifteen =