Gwamnan Zamfara ya kwace takardun gonaki da filaye wadanda aka bayar a guraren kiwo

88

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya kwace takardun mallakin gonaki da filaye wadanda aka bayar a guraren kiwo da aka warewa makiyaya a jihar, daga shekarar 1999 zuwa yanzu.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan Mallam Yusuf Idris, ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Gusau.

Yusuf Idris yace matakin gwamnan ya zama tilas domin kawo karshen rikicin makiyaya da manoma, wanda ake kyautata zaton yana da alaka da rabon gonakin da filayen kiwon.

Yace gwamna Matawalle ya kuma amince da kafa wani kwamitin da zummar shawo kan tashe-tashen hankulan da rabon gonaki ke haifarwa a jihar.

Daga nan sai yace za ayi sabon rabon da zarar kwamitin ya kammala aikinsa kuma ya mika rahotonsa ga gwamnati.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seven + twelve =