Fadar Shugaban Kasa tace hukuncin da gwamnatin Amurka ta dauka na saka Najeriya a cikin kasashen da ake sakawa ido, bazai mayar da Najeriya cikin kasashe masu fama da rashin yancin addini ba.
Da yake zantawa da manema labarai a kan lamarin, kakakin shugaban kasa Mallam Garba Shehu, yace kasashen Najeriya da Amurka za su tattauna akan lamarin, farkon shekara mai zuwa.
A cewarsa, saka Najeriya cikin kasashen da za a sakawa ido babu wani abu da zai haifar, kuma bazai mayar da kasar abar damuwa ba, kamar yadda wasu suke rade-radi.
Kakakin na shugaban kasa ya jaddada cewa Najeriya a matsayinta na kasa mai cin gashin kai, bata da wani kuduri na dora wani addini akan wani.
A cewar Garba Shehu, akwai yancin yin addini ga dukkanin yan kasa a kudin tsarin mulkin kasarnan.
Gwamnatin Amurka a satin da ya gabata aka rawaito ta sanya Najeriya cikin kasashen na musamman da ake sanyawa idanu wadanda suke dakile yancin addini.