Pantami ya yi kira da a marawa gwamnati baya wajen cimma manufar tattalin arziki na na’ura mai kwakwalwa

94

Minstan Sadarwa da Tattalin Arziki, Dr. Isa Ali Pantami, yayi kira ga masu ruwa da tsaki a fadin kasarnan da su marawa gwamnati baya wajen cimma manufar tattalin arziki na na’ura mai kwakwalwa ga ‘yan kasarnan zuwa shekarar 2023.

Isa Pantami yayi kiranne yayin bude taron shekara-shekara na Najeriya a yanar gizo, da nuna fasaha tare da bayar da kyaututtuka wanda hukumar cigaban fasahar sadarwa ta kasa NITDA ta shirya, tare da hadin gwiwar hukumomin dake karkashin ma’aikatar a Abuja.

A cewar Dr. Pantami, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari wacce ta mayar da hankali akan fadada tattalin arziki, tabbatar da tsaro, da yakar rashawa, zatayi amfani da fasahar sadarwa wajen cimma wadannan manufofi.

Yace kokarin mayar da tattalin arzikin kasarnan zuwa na na’ura mai kwakwalwa ya sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauya sunan ma’aikatar sadarwa zuwa ma’aikatar sadarwa da tattalin arziki na na’ura mai kwakwalwa.

Shugaban hukumar cigaban fasahar sadarwa ta kasa, NITDA, Mallam Kashifu Inuwa, yayi nuni da cewa tattalin arziki na na’ura mai kwakwalwa ya sauya salon aikin gwamnati, domin kawo cigaba a tsarin aikin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty − 3 =