Manoma Alkama Za Su Noma Gona Mai Fadin Kadada Dubu 20 a Kano

285

Akalla gona mai fadin kadada Dubu 20 manoman alkama zasu noma a karkashin shirin lamuni na manoma a jihar Kano a ranin bana.

Shugaban kungiyar manoma alkama na kasa reshen jihar Kano, Alhaji Musa Shehu Sheka, shine ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a Kano.

Shehu-Sheka yace kungiyar tayiwa manoma Dubu 15 rijista a karkashin shirin domin ranin bana, inda yace tuni aka aika da sunayensu zuwa babban bankin kasa CBN domin tantancewa.

Yace manoma sun fara share gonakinsu a shirye-shiryen fara shuka wanda aka sa ran farawa kowane lokaci daga yanzu har ya zuwa karshen watan gobe na Dismanba.

Shugaban kungiyar sai ya yabawa gwamnatin tarayya bisa shawararta na rufe iyakokin kasarnan, inda yayi nuni da cewa matakin ya karfafawa manoma dayawa gwiwa, wadanda suka dawo harkar, bayan a baya sun watsar da noman alkamar saboda rashin kasuwa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twelve − 9 =