Gwamnatin Jihar Jigawa ta sami lambar yabo a matsayin ta 1 a Najeriya a bangaren kasafin kudi a bayyane wanda bankin duniya ya gabatar.
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar shine ya bayyana hakan bayan ya rattaba hannu a kasafin kudi na 2020 a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse.
A cewarsa, Jigawa ta sami wannan nasara ne sakamakon ta sami maki kashi 87 inda jihar Kaduna wadda ke biye da ita ta sami kashi 60 kacal.
Haka zalika, Gwamnan ya yabawa kakakin majalisar Jihar Jigawa, Alhaji Idris Garba Kareka, da kafatanin ‘yan majalisar da suka yi kokarin kammala aikin kasafin kudi a cikin lokaci kankani.
Ya kara da cewa, kasafin kudin biyo bayan aikinsa da akayi a gurguje wanda ba’a taba hakan ba a tarihin jigawa, za a fara aiwatar dashi da zarar an shiga farkon shekara ta 2020.
A jiya ne Majalisar Dokoki ta Jihar Jigawa ta amince da dokar kasafin kudin gwamnatin jiha na sabuwar shekara ta 2020 na fiye da naira miliyan dubu 152 da miliyan 920 tare da wasu ‘yan gyare-gyare.