Tsohon malamin Jami’a ya zama sabon shugaban Tunisia

70
Kais Saied

Alkalumman da aka tattara tun bayan zaben shugaban kasar Tunisia na nuna cewa tsohon malamin shari’a Kais Saied ya lashe zaben da gagrumin rinjaye inda ya samu sama da kashi 70 cikin 100 na kuri’un da aka kada.

Mista Saied dan shakaru 61 da haihuwa ya fafata da wani dan kasuwa ne mamallakin kafofin sadarwa mai suna Nabil Karoui dan shekaru 56.

A lokacin yakin neman zabensa, Mista Saied, duk da karancin gogewa da yake dashi a siyasa ya maida hankali kan yakar cin hanci da kuma maido da martabar kasarsa a idon duniya.

A yayin wani gangami da magoya bayan Saied suka shirya, sabon shugaban ya gode masu domin damar da suka abshi ya jagoranci kasar, inda yace tare zasu yi aikin sake gina kasar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

8 + 17 =