Za’a kwaso ‘yan Nijeriya kyauta daga Afrika ta Kudu

70

Kamfanin zirga-zirgan jiragen sama na Air Peace yayi tayin kwaso ‘yan Nijeriya daga kasar Afrika ta Kudu don dawowa gida kyauta .

Babbar Jami’ar gudanarwan kamfanin Uwargida Oluwatoyin Oladije ce ta bayyana haka acikin wata wasika da ta aikewa ministan harkokin kasashen wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama a ranar Laraba.

Olajide ta bayyana abinda ya faru a matsayin abin takaici, inda tace “ba zamu zuba ido mu kalli ana kashe ‘yan Nijeriya a kasar Afrika ta kudu ba”. Jami’ar gudanarwan ta bayyana cewa kamfanin Air Peace zai taimakawa gwamnatin Nijeriya inda zasu tura jirgi samfarin kirar boyin 777 zuwa Afrika ta Kudu don kwaso ‘yan Nijeriya zuwa gida.

Hare-haren da aka kaiwa ‘yan kasashen ketare a rikicin nuna kin jinin baki na baya-bayan nan a shaguna da wuraren sana’a a Afrika ta kudu ya tunzura ‘yan Nijeriya matuka gaya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seven + 19 =