Kasar Afrika ta Kudu ta rufe ofishoshin jakadancinta da ke Nijeriya sakamakon hare-haren ramuwar gayya da ‘yan Nijeriya ke kaiwa ‘yan kasar Afrika ta Kudun, kamar yadda mukaddashin jakadan kasar a nan Nijeriya Bobby Moroe ya bayyana da safiyar yau.
Moroe yace hare-haren da ake kaiwa ‘yan kasar sa sune suka tilasta rufe ofishoshnsu har sai kura ta lafa.
“ Na bada umurnin rufe ofishoshin jakandancinmu har sai kura ta lafa. Mun samu labarin yadda ake kaiwa yan Afrika ta Kudu hari”
A baya dai, SkyDaily Hausa ta bada rahoton yadda aka rika kai hare-hare a kamfanoni mallakar kasar Afrika ta Kudu a Nijeriya, da kuma dawo da jakandan Nijeriya a kasar Afrika ta Kudu ya shugaba Muhammadu Buhari yayi a wani mataki na nuna bacin ran gwamnatin Nijeriya kan yadda aka kasha ‘yan kasarta a rikin kyamar baki da ya farau a wannan satin acan kasar ta Afrika ta Kudu