Sudan: An nada sabbin ministoci

36
Abdallah Hamdok

A karon farko bayan an kulla yarjejeniya tsakanin fararen-hula da sojoji a Sudan, firai ministan kasar Abdalla Hamdok ya bayyana nada sabbin ministoci 18 da zasu mulki kasar.

A wajabin da firai ministan ya gabatar a babban birnin kasar Khartoum, Hamdok ya bayyana cewa babban burinsu a halin yanzu shine samar da zaman lafiya tare da kawo karshen yaki a Sudan.

Acikin ministocin da aka nada akwai mata guda hudu, ciki har da Asma Mohamed Abdalla a matsayin ministan harkokin kasahen waje. Haka kuma an nada tsohon jami’in bankin duniya Ibrahim Elbadawi a matsayin ministan kudi, ya yinda sojoji zasu kula da ma’aikatun tsaro da na harkokin cikin gida.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seventeen − fifteen =