Hisbah ta fasa kwalaben barasa 196,400 a Kano

185

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta fasa kwalaben barasa 196,400 da ta kama a cikin garin kano.

Bayanin haka ya fito ne acikin wata sanarwa da kakakin mataimakin gwamnan kano Hassan Musa Fagge ya sanya wa hannu.

A lokacin da yake jawabi jim kadan da kamala fasa kwalaben barasan a karamar hukumar Dawakin Tofa, gwamna Abdullahi Ganduje yace addinin musulunci ya haramta shan barasa da ta’ammali da ita, da kuma abubuwan da ke sanya maye da bugarwa wandanda zasu iya yin illa ga kwakwalwa.

Addinin musulunci ya hana shan barasa, malamanmu na addinin musulunci da shugabanninmu su hada hannu domin yakan wannan matsalar ta shaye-shaye” inji Ganduje.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × 3 =