Buhari zai halarci taron kasashen yammacin Afrika a Burkina Faso

91
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buahri zai halarci taron shugabannin kasashen yammacin Afrika da za’ayi a Burkina Faso don tattauna yadda zasu shawo kan aikin ta’addanci.

Mai baiwa shugaban kasa shawara ta fannin yada labarai Femi Adesina ya bayyana haka acikin wata sanarwa da ya fitar jiya Jumma’a a Abuja.

Taron wanda zai gudana a yau Asabar zai maida hankali ne kan dabarun yaki da ta’addanci a kasashen yankin Sahel, kuma zai hada da dukkan shugabannin kasashen kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS)

Ana sa ran taron zai duba ayyukan da rundunar tsaro ta G5 Sahel ta yi da kuma sauran manyan batutuwa da suka shafi tsaro.

Buhari zai samu rakiyar mukarrabn gwamnati zuwa Burkina Faso, wadanda suka hada da Gwamna  Abubakar Bello na Jihar Niger, Dafo Abiodin na Ogun, da kuma Okezie Ikpeazu na Abia.

Sauran yan rakiyar sun hada da Ministan tsaro Bashir Magashi, Ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyenma, maibada shawara ta fannin tsaro Babagana Manguno da kuma darakata janar na hukumar lekan asiri Ahmed Abubakar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × five =