Shugaba Buhari ya Rantsar da Shugaba da Mabobin Hukumar Kula da Majalisun Kasa

43

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Injiniya Ahmed Kadi Amshi da wasu mutane 11 a matsayin shugaba da mambobin hukumar kula da majalisun kasa.

An gudanar da bikin kaddamarwar a zauren fadar shugaban kasa dake Abuja.

Sabon shugaban hukumar kula da majalisar, Ahmed Kadi Amshi, yana wakiltar jihar Yobe ne, a Arewa maso Gabas.

Sauran mambobin hukumar sune Babagana Modu, Jihar Borno, Arewa maso Gabas; da Abubakar Tutare, Jihae Taraba, Arewa maso Gabas; da Hakeem Akamo, Jihar Lagos, Kudu Maso Yamma; da Tunrayo Akintomide, Jihar Ondo, Kudu Maso Yamma.

Sauran sune Bassey Etuk, Jihar Akwa-Ibom, Kudu Maso Kudu; da Bailyaminu Yusuf Shinkafi, Jihar Zamfara, Arewa Maso Yamma; da Sani Saidu Kazaure, Jihar Jigawa, Arewa Maso Yamma; da Julius Ucha, Jihar Ebonyi, Kudu Maso Gabas; da Auwalu Aliyu Ohindase, Jihar Kogi, Arewa ta Tsakiya, da Muazu Is’haq, Jihar Nasarawa, Arewa ta Tsakiya  da kuma Atanomeyorwi Francis, Jihar Delta, Kudu Maso Kudu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eleven + 11 =