Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Bukaci Iyaye Da Su Kai Yaransu Makaranta Ko Su Fuskanci Hukunci

29

Gwamnatin Jihar Kaduna ya shawarci iyaye da su kai yayansu makaranta ko kuma su fuskanci hukunci kamar yadda ake a doka.

Babban sakatarariyar hukumar ilimi ta jihar, Mrs Phoebe Yayi, ta bayar da shawarar a Kaduna yayinda take zantawa da manema labarai.

Phobe Yayi ta jaddada cewa kowane yaro ko yarinya suna da hakkin ilimin bai daya wanda yake kyauta kuma tilas, inda ta kara da cewa gwamnatin jihar ce ke da alhakin samar da ilimin.

Tace a kokarin sauke nauyin dake wuyanta, gwamnatin jihar ta ayyan cewa ilimi ya zama kyauta ga kowa da kowa daga matakin firamare zuwa sakandire a jihar.

Babbar sakatariyar ta bayyana cewa matakin wani bangare ne wajen tabbatar da cewa dukkan mazauna jihar sun samu ilimi wanda zai basu damar gudanar da rayuwa mai inganci.

Ta kuma yi gargadin cewa babu dalilin da zai sa iyaye su hana ‘ya’yansu zuwa makaranta, lamarin da zai sa yaran su samu rayuwa mai inganci a gaba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 + twenty =