Shugaban kasa Muhammad Buhari, yabar birnin tarrayya Abuja domin zuwa Birnin London na kasar Birtaniya, domin halartar kaddamar da taron bunkasa kasuwanci tsakanin kasar Burtaniya da Kasashen Afrika wanda za’ayi a ranar 20 ga watan Janeru.
Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya rawaito cewa shugaban Buhari kafin Tafiyar tasa sai da ya gudanar da ganawar sirri da hafsoshin tsaron na kasa a fadarsa dake Abuja.
Haka kuma Shugaba Buhari yabi sahun Daruruwan Musulman kasar, domin gudanar da Sallar Juma’a a cikin masallacin dake fadar shugaban kasa.
Cikin wata sanarwa da Mai Taimaka Masa ta kafafen yada labarai Femi Adesina, ya rabawa manema labarai, a Abuja, ya ce Firaministan Kasar Burtaniya wato Boris Johnson shine zai kasance mai masaukin baki.
Kazalika ya ce taron wanda Wakilan Nijeriya zasu halarta, shine yake nuna cewa Gwamnatin tarrayya tayi wasu sabbin tsare-tsare wanda hakan zai bunkasa harkokin kasawanci da kuma sauyin yanayi a fadin kasar nan. Ana saran shugaba Buhari zai dawo gida Nijeriya a ranar Alhamis.