Burutai ya Kaddamar da Sabon Gini a Jami’ar Sojoji ta Biu a Jihar Borno

153

Shugaban Sojojin Nijeriya Laftar Janar Tukur Burutai ya kaddamar da sabon ginin da aka ginawa tsangayar kimiyya na Jami’ar Sojoji dake Biu a jihar Borno.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya rawaito cewa, an kafa jami’ar ne a shekarar 2017, inda kuma jami’ar ta fara daukan dalibai 1,000 a shekarar 2018, wanda suka fara karatu a fannoni daban-daban.

Sabon ginin da aka gina a tsangayar ya hada da ofisoshi 47 na malaman makarantar ciki harda ofishin shugaban tsangayar da na mataimakinsa da kuma ajujuwan dalibai guda 24 tare da dakunan gwaje-gwaje guda 3.

Da yake kaddamar da sabon ginin, Tukur Burutai, ya bayyana cewa sabon ginin yana daya daga cikin sabbin gine-gine da ake ginawa a cikin Jami’ar wanda hukumar soji da gwamnatin tarrayya ke ginawa.

A cewarsa, manufar kafa Jami’ar shine, domin ta magance matsalolin rashin guraren gudanar da bincike da kuma bunkasa fasaha wajen warware matsalolin da Nijeriya ke fama dasu da kuma hukumar sojin kasar, tare da samar da hanyoyin dagaro da kai.

NAN

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × 1 =