Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano Ta Yi Nasarar Ceto Rayuka 1,055 a 2019

26

Hukumar Kashe Gobara ta jihar Kano ta ce tayi nasarar ceto rayuka 1,055 da dukiyoyi masu yawa, wanda kudinsu yakai kimanin Naira Biliyan 1 da Miliyan 900 cikin rahoto 813 na gobara da hukumar ta samu daga watan Janeru zuwa Disamba na 2019 da ta gabata.

Jami’in hulda da Jama’a na hukumar Alhaji Saidu Muhammad shine ya bayyana haka cikin wata tattaunawa da manema labarai a jihar Kano.

Haka kuma ya ce kimanin rayuka 111 ne suka salwanta a lokutan da Infila’in ya faru.

Kazalika ya ce kimanin kadarorin da suka kai Naira Miliyan 679 ne suka salwanta, a yayinda hukumar ta sami kiraye-kiraye sau 744, haka kuma sun sami kiraye-kiraye na karya guda 180.

Alhaji Saidu Muhammad ya ce mafiya yawa daga cikin gobarar ta faru ne sakamakon sakaci da wutar lantarki, da Gas din Girki da kuma yin amfani da Na’urar Girki ta hanyar da bata dace ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × 4 =