Karamar Hukuma a Jigawa Ta Hana Maza da Mata Yin Fira da Dare

60

Karamar Hukumar Kirikasamma a nan jihar Jigawa ta zartar da dokar hana maza da mata yin fira da daddare.

Karamar hukumar tace hakan yazo ne sanadiyyar yawaitar yin ciki ba tare da aure ba, da yanmata ke yi.

Jami’in yada labarai na karamar hukumar, Sanusi Doro, yace shugaban karamar hukumar, Salisu Kubayo, ya sanya hannu akan dokar bayan kamsilolin karamar hukumar su 10 sun amince da ita, yayin zaman majalisar karamar hukumar.

Dangane da sabuwar dokar, matukar namiji da mace, ko da saurayi da budurwarsa ne, aka kama suna fira, za a yanke musu hukuncin zaman gidan yari na watanni 6, ko kuma zabin biyan tara ta kudi Naira Dubu 50.

Jami’in yada labaran yace masoya na gaskiya zasu iya ganawa ne kadai da hasken rana.

An gudanar da sanya hannu akan dokar a wani biki wanda jama’ar garin suka hallara sosai, cikinsu har da babban limamin garin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nineteen − 16 =