Daruruwan mutane ne a tsakiyar birnin Algiers na Aljeria suka hallara a wata zanga-zanga mai girma dan matsawa hukumomin kasar su soke zaben da yake gabatowa.
Ana gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati kowace ranar Juma’a da Talata, tun cikin tsakiyar watan Fabrairu, kuma zanga-zangar ce ta jawo dadadden shugaban kasar, Abdul’aziz Bouteflika yayi murabus a watan Afrilu.
Tun daga wancan lokacin, masu zanga-zanga suke bukatar manyan kusoshin gwamnatin Bouteflika su ajiye aiki, tare da garanbawul a tsarin siyasar kasar, kafin a gudanar da zaben shugaban kasa.
Jiya Alhamis, kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty tayi gargadin cewa hukomimi a kasar ta Aljeriya sun zafafa kame da azabtar da masu zanga-zanga cikin makonninan.