Tsohon Shugaban Kasar Ghana Ya Roki Gwamnatin Najeriya Ta Bude Iyakokinta Saboda Harkokin Kasuwanci Su Dawo a Yankin Afirka Ta Yamma

49

Tsohon shugaban kasar Ghana, Mista John Mahama, ya roki gwamnatin Najeriya ta bude iyakokinta saboda harkokin kasuwanci su dawo a yankin Afirka ta yamma.

John Mahama yayi wannan rokon ne yayin da yake gabatar da wata lakca tare da kaddamar da littafi akan hanyoyin cigaban  siyasa da tattalin arziki a nahiyar Afirka, wanda aka gudanar a Lagos.

Yace rufe iyakokin kasarnan, musamman na kasar Benin, na matukar shafar kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa musamman a kasashen Togo da Ghana da Kwadebuwa, wadanda suka dogara da kasuwanci tsakanin kasa da kasa.

John Mahama yace a matsayinsa na tsohon shugaban hukumar raya tattalin arzikin Afirka ta yamma, ECOWAS, yana da sha’awar cigaban hukumar ta ECOWAS da mutanenta.

Yace amfani da fasahar zamani zata bayar da dama ga nahiyar ta kara yawan kayan da take sarrafawa tare da ‘yanta karin mutanen dake aikin wahala ta hanyar basu damar samun ayyuka daban-daban.                                                                   

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × one =