Mai kamfanin Twitter Jack Dorsey ya bayyana aniyar kamfaninsa na dakatar da tallan da ya shafi duk wani dangi na siyasa a fadin duniya.
Mista Dorsey ya bayyana haka ne a wani sakon twitter da ya wallafa a shafinsa, in da yace yyain da kafafen internet ke karfi kuma ‘yan kasuwa ke amfani dashi dan yin talla a duniya, hakan a cewar Jack nayin barazana ga siyasa.
Kafafen sada zumunta dai na fuskantar kalubale na tsaro a gabanin zaben shugaban kasar Amirka na shekarar 2020.
A bayadai kamfanin Facebook wanda abokin takarar Twitter ne ya dauki matakin haramta tallan ‘yan siyasa da duk wani talla da ya shafi siyasa.
Dorsey ya bayyana cewa haramcin zai fara ne daga ranar 22 ga watan Nuwamna na wannan shekarar, yayin da za’a fitar da bayanin yadda tsarin zai kasance a ranar 15 ga watan Nuwamba na 2019.