Saƙon da Mahamat Deby ya ce mu faɗa wa Tinubu game da Boko Haram – Ribadu

8

Gwamnatin Najeriya ta ce tana kan tattaunawa da takwararta ta Chadi game da aikin haɗin gwiwa a yaƙi da ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi a yankin Tafkin Chadi.

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya faɗa wa BBC cewa ya jagoranci tawagar ta’aziyya zuwa ga Shugaban Chadi Mahamat Idris Deby kan sojojinsa da ƙungiyar Boko Haram ta kashe a baya-bayan nan.

Kisan sojojin kusan 40 ya sa Shugaba Deby ya yi barazanar ficewa daga rundunar Mutlinational Joint Taske Force (MNJTF) yayin da ya kai ziyara sansanin Barkaram – wani tsauni da ke yankin na Tafkin Chadi.

“Mun kai saƙo ne daga shugabanmu Bola Tinubu, ya ba mu takarda mu kai wa shugaban Chadi domin mu jajanta masa saboda duk abin da ya samu Chadi ya shafi Najeriya,” a cewar Nuhu Ribadu.

Ƙasashen Najeriya, da Nijar, da Chadi, da Kamaru, da Benin ne ke yin karo-karon dakaru a rundunar, kuma masana na cewa barazanar da shugaban Chadi ya yi ka iya yin illa ga ƙungiyar mai shekara 10 da kafuwa.

Ribadu ya ce sun shafe kusan awa uku suna tattaunawa da shugaban na Chadi.

“Mun yi maganganu masu ma’ana ƙwarai, kuma za mu zauna da Shugaba Tinubu domin duba abubuwan da ya faɗa mana, amma dai abin bai kai a ce za su janye ba. Za mu ƙara gyarawa.”

BBC HAUSA

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five + sixteen =