Zaben 2019: Kotun daukaka kara ta soke zaben da akayima yan majalisun tarayya guda biyu na jam’iyar APC

110

Kotun daukaka kara ta soke zaben da aka yiwa ‘yan majilasar tarayya guda biyu daga jihar Sokoto a zaman da tayi jiya Laraba.

Kotun ta soke zaben da akayi wa Sanata Abubakar Shehu Tambuwal na jam’iyar APC da maye gurbinsa da dan takarar jam’iyar PDP Ibrahim Danbaba.

Haka kuma kotun ta soke zaben dan majalisar tarayya mai wakiltar Bodinga/Dange Shuni/Tureta inda ta maye gurbinsa da Balarabe Kakale na jam’iyar PDP.

A cikin wata sanarwan da jam’iyar APC ta rabawa manema labarai dangane da hukuncin kotun ta bakin shugabanta Alhaji Sadiq Acida, ta umurci magoya bayansu da su kwantar da hankilinsu, inda sukace zasuyi nazari kan hukuncin tare da bayyana matsayinsu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 − eighteen =