RANAR 14 GA MARIS SHUGABA TINUBU NA NAJERIYA ZAI KADDAMAR DA SHIRIN BADA LAMUNIN KARATU GA DALIBAN KASAR

6

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kaddamar da shirin bada lamunin kudin karatu ranar Alhamis 14 ga wannan wata.

Hadimin shugaban kasa a kafafan yada labarai Mista Ajuri Ngelale shine ya sanar da haka a gidan Talabijin na TVC.

Idan za’a iya tunawa ranar 12 ga watan Yulin shekarar 2023 shugaban kasa Tinubu, ya sanya hannu kan dokar bada rancen kudin karatu maras ruwa domin bawa daliban kasar nan damar yin karatu a manyan makarantun gaba da sakandire.

Dokar wacce aka fi sani da dokar lamunin kudin karatu ga dalibai,an samar da asusun bada rancen kudin karatu ga daliban Najeriya,wacce za’a na karbar rance da tallafin karatu da kuma maida kudin da aka ranto.

Da farko gwamnati tace shirin zai fara a watan Nuwamba amma bai fara ba,daga bisani aka dage zuwa watan Janeru shima dai bai fara a watan ba.

Shugaban kasa ya ware Naira bilyan 50 daga cikin kasafin kudin shekarar 2024 da ya gabatar a gaban majalisar dokokin kasar nan domin fara shirin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × 4 =