SARKIN MUSULMI YA BADA UMARNIN A FARA DUBAN WATAN RAMADAN A GOBE LAHADI

27

Majalisar Koli ta harkokin addinin Musulunci ta Najeriya, karkashin jagorancin mai alfarma sarkin Musulmi Alh Muhammad Sa’ad Abubakar na uku, ta bukaci Musulmi a fadin kasar nan da su fara duban watan Ramadan na wannan shekarar ta 1445 a gobe Lahadi.

Mataimakin sakataran majalisar Farfesa Salisu Shehu shine ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar jiya.

A cewar sa, Mai Alfarma Sarkin Musulmi yana taya daukacin Musulmi murnar zuwan watan Ramadan.

Majalisar kolin ta harkokin addinin musulunci ta kasa ta yi addu’ar Allah ya kai rayuwar kowanne Musulmi ta riski watan Ramadan da kuma samun damar yin Ibada a cikin watan.

La’akari da halin matsin rayuwa da matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta, Sarkin Musulmi ya bukaci musulmi su fadada ayyukan su na neman lada da tallafawa mabukata da makwabta a lokacin watan azumin.

Majalisar ta kuma gargadi ‘Yan kasuwa da su kauracewa taskance kayan abinci da tsawwala farashin kayayyaki yayin Azumin watan Ramadan.

Alh Sa’ad Abubakar na uku, ya bukaci Musulmi su yi amfani da wannan wata mai alfama wajen yin Addu’o’I Allah ya taimaki Falasdinawa kan makiyan su.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × five =