Abin kunya ne Buhari ya mika mulki ga ‘yan adawa – Adamu

19

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, yace abin kunya ne ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika mulki ga jam’iyyar adawa a shekarar 2023.

A wata ganawa da BBC Hausa, shugaban jam’iyyar yace shugaban kasa Muhammadu Buhari bashi da wani buri da ya wuce yaga APC ta samu nasara.

Da yake watsi da sukar dake zargin cewa Shugaba Buhari yana janye jikinsa daga zuwa gangamin yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Abdullahi Adamu yace ba abu ne da ya dace ba ya bar aikinsa na shugaban kasa domin yakin neman zabe.

Akan sukar cewa Shugaba Buhari ya janye jikinsa daga gangamin jam’iyyar, Abdullahi Adamu yace ba gaskiya bane.

Dangane da yawan jama’a da sauran jam’iyyun siyasa ke tarawa a gangamin yakin neman zabe, shugaban jam’iyyar yace APC bata tsoron komai.

A wani labarin kuma, Kungiyar yakin neman zaben Atiku/Okowa tace dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, zai lashe zaben shugaban kasa a zagayen farko.

Kakakin kungiyar, Kola Ologbondiyan, ya bayyana kwarin gwiwar cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja.

Kola Ologbondiyan yace da dumbin goyon bayan da ‘yan Najeriya ke bawa Atiku Abubakar a ko’ina a fadin kasarnan, sakamakon zaben shugaban kasar, wanda Atiku Abubakar zai lashe a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, zai girgiza masu hasashen jin ra’ayin jama’a.

Kola Ologbondiyan ya kara da cewa a bayyana yake cewa babu wani dan takara da yake da karfi da karbuwa a ko’ina a kasarnan da zai iya kayar da Atiku Abubakar a zagayen farko.

Ya bukaci ‘yan Najrriya da su cigaba da hada kai tare da mayar da hankali wajen marawa Atiku Abubakar baya a kokarin ceto kasarnan da sake gina ta.

A halin da ake ciki kuma, domin karkare yarjejeniyar zaben shugaban kasa na shekarar 2023, gwamnonin jam’iyyar PDP guda 5 da aka batawa rai na shirin ganawa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Wata majiya mai tushe ta kusa da tsohon gwamnan jihar Lagos tace indai ba wani canji aka samu a kurarren lokaci ba, za a gudanar da zaman ganawar a daya daga cikin kasashen Turai a wannan makon.

Majiyar wacce ta ki bayar da tsayayyar ranar zaman ganawar, sai dai tace an shirya zaman domin cimma yarjejeniya akan zaben shugaban kasa na 2023 tare da gwamnonin.

Yace bayan zaman ganawar, gwamnonin 5 na PDP da suka hada da Nyesom Wike na jihar Rivers da Seyi Makinde na jihar Oyo da Samuel Ortom na jihar Benue da Okezie Ikpeazu na jihar Abia da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, za su sanarwa jama’a dan takarar shugaban kasar da za su marawa baya.

Gwamnonin, an ruwaito cewa tuni suna Birtaniya gabannin zaman ganawar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 − sixteen =