Kolmani: Babu sabani tsakanin Bauchi da Gombe – Sarkin Gombe

33

Mai Martaba Sarkin Gombe, Abubakar Shehu Abubakar, yace babu wani sabani tsakanin jihohin Gombe da Bauchi dangane da sansanin man fetur na Kolmani.

Ana samun rashin jituwa dangane da mallakin sansanin na man fetur tsakanin wasu al’umomin jihohin Gombe da Bauchi, biyo bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin hakar man fetur na Kolmani a watan Nuwamban da ya gabata.

Da yake magana jiya yayin ziyarar godiya ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari daga wata tawagar ‘yan siyasa da shugabannin addini da na ‘yan kasuwar jihar Gombe a fadar shugaban kasa dake Abuja, Sarkin yace jihohin biyun ‘yan uwan juna ne wadanda ke da tarihi guda.

Da yake mayar da martani, shugaban kasar yace lokacin da ya rike mukamin ministan man fetur tsawon shekara uku a shekarun 1970, ma’aikatar ta gudanar da bincike, tare da amannar cewa za ta kawo daidaito kan batun.

Jagoran tawagar, gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, yace mutanen Gombe sun zo su bayyana dumbin godiyarsu bisa kaddamar da aikin hakar mai na Kolmani.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 − 8 =