PDP ta sha alwashin kwace mulkin Jigawa a 2023

29

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP reshen jihar Jigawa ta sha alwashin kawo karshen mulkin jam’iyyar APC a babban zaben 2023 mai zuwa a jihar.

Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar, Mustapha Sule Lamido, ya sanar da shirin jim kadan kadan bayan gabatar da tutocin takara ga ‘yan takarkarun jam’iyyar PDP jiya a sakateriyar jam’iyyar ta jiha da ke Dutse.

Mustapha Lamido wanda ya dauki alkawarin ayyana dokar ta baci a bangaren daukar matasa aiki daban-daban, yace lokaci yayi da matasan jihar Jigawa za su zama masu dogaro da kawunansu.

A cewarsa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, shima yayi alkawarin ganin cewa jihar Jigawa ta tsaya da kafufuwanta, ba tare da dogaro da kason gwamnatin tarayya ba.

Yace duba da yadda jam’iyyar APC mai mulki ta tura ‘yan Jigawa rayuwar yunwa da kunci, jam’iyyar PDP ce kadai jirgin fiton talakawa daga wadannan wahalhalun.

Mustapha Lamido ya yabawa dumbin jama’ar da suka halarci taron inda ya bukaci ‘yan Jigawa da su mara masa baya domin kaiwa ga gaci a zaben na badi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 + ten =