Kotu ta bayar da umarnin kama babban hafsan sojin kasa

18

Wata babbar kotun jihar Neja a Minna, babban birnin jihar, ta bayar da umarnin kama baban sojin kasarnan, Janar Faruk Yahaya, bisa laifin raina kotu.

Mai shari’ah Halima Abdulmalik, wacce ta jagoranci shari’ar, tace umarnin ya biyo bayan karar da aka kawo katun bisa tanadin doka ta 42 hukunci na 10 na dokokin babbar kotun jihar Neja na shekarar 2018.

Ta kuma bayar da umarnin kama Kwamandan barikin horas da sojoji dake Minna, Olugbenga Olabanji, bisa irin laifin.

An bayar da umarnin ne bisa shari’ar da ake yi tsakanin Adamu Makama da wasu mutane 42 a hannu dayan, da kuma gwamnan jihar Neja da wasu mutane 7 a daya hannun.

Lauyan wadanda suka shigar da karar ne, Mohammed Liman, ya bukaci kotun ta bayar da umarnin kama su.

Mohammed Liman ya nemi kotun da ta aika da babban hafsan sojin kasa da kwamandan zuwa gidan yari bisa kin bin hukuncin da ta yanke a watan Oktoba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

20 + 20 =