Gwamnatin Tarayya ta ayyana cewa Najeriya ba ta talauce ba

27

Gwamnatin tarayya ta ayyana cewa Najeriya bata talauce ba kuma za ta iya biyan dukkan basussukan da ake binta a gajere, matsakaici da dogon zango.

Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, ta sanar da haka yayin da take jawabi akan nasarorin ma’aikatarta cikin shekaru 7 da suka gabata, yau a Abuja.

Ta yi nuni da cewa duk da kasancewar gwamnatin tarayya bata samun isassun kudade, ana samun cigaba a kudaden shiga, inda ta kara da cewa an samu raguwar satar danyen mai.

A wani labarin mai alaka da wannan, ministan sadarwa da tattalin arzikin digital, Isa Ali Pantami, yace bangaren fasahar sadarwa yana taimakawa sosai ga ma’aunanin tattalin arzikin kasa na GDP na kasarnan, inda ya bayar da gudunmawar kashi 18.44 a tsakiyar shekarar 2022.

A cewar ministan, bangaren fasahar sadarwa ya karu da kashi 14.70 a karshen shekarar 2020.

Yace hakan ya sanya bangaren ya zama mafi samun cigaba a tattalin arzikin Najeriya a karshen shekarar ta 2020.

A wani labarin kuma, gwamnatin Tarayya tace bisa la’akari da tarin kudi naira tiriliyan 5 da miliyan dubu 30 da kuma dalar Amurka miliyan dubu 3 da miliyan 400 da aka rabawa jihohi a matsayin tallafin cikin shekaru 7, babu wata gwamnati da ta taimakawa jihohin fiye da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed da ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, sune suka sanar da haka yau a Abuja a karo na 6 na taron shelar ayyukan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Matsayar ta gwamnatin tarayya na zuwa ne kasa da awanni 24 bayan ta zargi gwamnonin jihohi 36 da rashin mayar da hankali kan ayyyukan da ke taimakawa wajen rage talauci, duk da dumbin kudaden tallafin da gwamnatin tarayya ke ba su.

A jawabinsa na bude taro, Lai Mohammed yace tun daga shekarar 1999, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu ta fi kowace gwamnati kokari wajen tallafawa jihohi ta hanyoyi daban-daban domin rage talauci, biyan albashi da sauransu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twelve − four =