Kotu ta tabbatar da Aishatu Binani a matsayin ‘yar takarar gwamnar Adamawa

50

Wata kotun daukaka kara da ke zamanta a Yola, babban birnin jihar Adamawa, ta bayyana Sanata Aishatu Dahiru Binani a matsayin ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Adamawa.

Kotun karkashin mai shari’a Tani Yusuf Hassan ta yi watsi da hukuncin wata babbar kotun tarayya da ta soke zaben fidda gwani na gwamnan tare da bayyana cewa APC ba ta da dan takarar gwamna a zaben 2023.

Tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Malam Nuhu Ribadu, wanda ya tsaya takara amma ya fadi zaben fidda gwanin, ya kalubalanci nasarar Aishatu Binani a kotu.

Nuhu Ribadu ya shigar da kara ne domin neman a soke zaben fidda gwanin da aka gudanar a ranar 27 ga watan Mayu.

Nuhu Ribadu, wanda ya assasa kararsa kan zargin sayen kuri’u, da yawan kuri’un zaben da kuma sayen wakilai, ya bukaci kotu da ta soke Aishatu Binani tare da bayyana shi a matsayin ‘yar takarar jam’iyyar APC a jihar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × 3 =