Gwamnatin Tarayya ta haka burtsatse 150 a Adamawa

21

Gwamnatin tarayya ta ce ta hako rijiyoyin burtsatse guda 150 domin inganta samar da tsaftataccen ruwan sha a jihar Adamawa.

Kwanturola a ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya Aminu Sambo ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa, jiya a Yola, babban birnin jihar.

Ya ce gwamnati ta samar da rijiyoyin burtsatse da aka haka tare da tankunan ruwa na sama da kuma wuraren fitar da ruwa a kauyukan da ke fadin kananan hukumomi 21 na jihar, domin magance matsalar karancin ruwa.

Ya ce aikin ya shafi al’ummar karkara ne domin saukaka wahalhalun da mazauna karkara ke fuskanta wajen samun ruwa mai tsafta.

A cewarsa, gwamnatin tarayya ta kuma gina gidaje 100 tare da sanya fitillun kan titi guda 780 masu amfani da hasken rana a wasu zababbun kauyuka a fadin jihar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 + 18 =