Jigawa ta zama jiha ta farko da aka dena bahaya a sarari

52

Ministan Albarkatun Ruwa, Suleiman Adamu a jiya ya yabawa jihar Jigawa a matsayin jiha ta farko da ake dena bahaya a sarari, bayan ta cika dukkan sharudda da ka’idojin da aka gindaya.

Suleiman Adamu ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai na duniya a shirye-shiryen taron kolin bandaki na duniya na bana da za a yi a watan Nuwamba mai zuwa.

Ya ce Jigawa ta zama abar koyi kuma ta cancanci a yaba mata bisa jajircewarta wajen tabbatar da dena bahaya a sarari.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa, kafin a kai ga matakin tabbatar da dena bahaya a sarari, dole kauyuka su kawar da dabi’ar dena bahaya a sarari da kuma riko da tsarin tsaftar muhalli baki daya, wadanda suka hada da tsaftar jikin mutum, da ta muhalli da kuma cikin gida.

Ministan ya kuma yabawa kungiyar gangamin tsaftace Najeriya da Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, bisa jajircewar da suka yi wajen ganin an samar da kudin tabbatar da dena bahaya a sariri a Najeriya nan da shekarar 2025.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 + one =