NNPC ya sanya hannu akan yarjejeniyar gyaran matatar mai ta Kaduna

24

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana farin cikinsa a lokacin da ya shaida rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Kamfanin Mai na Kasa NNPC da wani kamfanin kasar waje mai suna Daewoo Group akan gyara matatar mai ta Kaduna.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar yau a Abuja.

Femi Adesina ya ce shugaban kasar ya yi matukar farin ciki da sanya hannun da kamfanin na Daewoo Group dake aikin gyaran matatar mai ta Warri.

A cewar hadimin shugaban kasar, aikin gyaran matatar mai ta Warri, idan aka kammala, za a fara tace mai kafin tsakiyar shekarar 2023.

Shugaban kasar ya ce yana sa ran ganin an kammala ayyukan da ake gudanarwa musamman a matatun man Warri da Kaduna.

A wani batun kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tunatar da ‘yan Najeriya mazauna kasar Koriya ta Kudu cewa su ne jakadun Najeriya, a saboda haka ya kamata su wakilci kasar yadda ya kamata.

Ya kuma bukace su da su yi kokarin fito da kyakkyawan yanayin kasar nan ta hanyar ayyukansu, halayensu, dabi’unsu da kuma maganganunsu gaba daya.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a yau yayin wata ganawar tattaunawa da wasu zababbun ‘yan Najeriya a wani bangare na ayyukan sa a karshen taron duniya na farko kan kiwon lafiya na bana a birnin Seoul.

Shugaban kasar ya bukace su da su ci gaba da zama jakadu nagari ga Najeriya a kowane lokaci.

Shugaba Buhari wanda ya ba su tabbacin cewa gwamnatin tarayya ta hannun ofishin jakadancin kasarnan, za ta ci gaba da kokarin kare muradunsu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eight − 1 =