Buhari ya amince da raba hatsi ga wadanda ambaliya ta shafa

26

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da raba ton dubu 12 na hatsi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a fadin kasar nan.

Darakta-Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Mustapha Habib Ahmed, ne ya bayyana hakan a Abuja jiya a yayin bikin Ranar Rage Hadarin Annoba ta Duniya na bana.

Ya ce hukumar NEMA tana kuma aikawa da kayan agaji.

Ya ce, duk da cewa ambaliyar da aka yi a Lokoja, jihar Kogi, na kawo tsaiko wajen aikawa da kayayyakin, amma an sanar da jami’an tsaro domin tabbatar da an yi nasarar isar da kayayyakin.

Mustapha Habib ya ce mummunar ambaliya a fadin kasar nan a wannan shekara ta auku ne saboda al’ummomi sun yi biris da gargadin farko kan ambaliyar.

Ya ce gwamnatin tarayya ta sanar da jahohi da kananan hukumomin game da hatsarin da ake fuskanta na ambaliya, tare da yin amfani da taswirori wajen gano wuraren da ambaliyar za ta iya shafa, amma ba a kula da gargadin ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

10 − 3 =