Jagoran addini a kasar Iran, Ayatullah Ali Khamenei, ya zargi Amurka da Isra’ila da hannu a zanga-zangar da ake yi a kasar biyo bayan mutuwar wata mata a hannun ‘yan hisbah.
A jawabinsa na farko a bainar jama’a dangane da zanga-zangar, Ali Khamenei ya ce manyan makiya Iran da kawayensu ne suka shirya tarzomar.
Zanga-zangar ita ce babban kalubalen da ya fuskanta a mulkinsa na tsawon shekaru goma, don haka ya bukaci jami’an tsaro da su kasance cikin shirin ko ta kwana.
Da yake jawabi a wajen bikin yaye daliban jami’an ‘yan sanda da na sojoji a jiya, shugaban addinin ya ce mutuwar Amsa Amini abin takaici ne.
Ayatullah Ali Khamenei ya tabbatar da cewa kasashen waje sun shirya tarzoma ne saboda ba za su lamunci yadda Iran ke samun karfi a dukkan bangarori ba.
Shugaban Amurka Joe Biden ya fitar da wata sanarwa yana mai cewa ya damu da rahotannin murkushe masu zanga-zanga.