Sojojin isra’ila sun kashe Falasdinawa 4 yayin wani sumame

40

Falasdinawa 4 ne aka kashe tare da jikkata wasu 44 a wani samame da sojojin Isra’ila suka kai a Jenin da ke gabar yammacin kogin Jordan da suka mamaye.

Jami’an kiwon lafiya na Falasdinu sun ce daya daga cikin wadanda suka mutu shi ne Abd al-Rahman Hazem, wanda dan uwansa ya harbe wasu ‘yan Isra’ila uku a birnin Tel Aviv a watan Afrilun bana.

Shaidun gani da ido sun ce an tashi bama-bamai da kuma harbe-harbe bayan da dimbin motocin sojojin Isra’ila suka shiga Jenin.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce dakarunta sun kewaye wani gida da nufin kame wasu mutane biyu da ake zargi da harbe-harbe.

Kafofin yada labaran Falasdinu sun rawaito cewa, sojojin sun harba makami mai linzami a gidan a lokacin da ake luguden wuta.

Sojojin Isra’ila da ma’aikatar lafiya ta Falasdinu duk sun ce Abd al-Rahman Hazem na daya daga cikin mutanen biyu da aka kashe a cikin gidan.

A cewar ma’aikatar lafiya, an harbe wasu Palasdinawa biyu a wani artabun sojojin Isra’ila da ya barke a sansanin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

ten − 2 =