Kotu tace Sule Lamido yana da tuhumar da zai amsa

108

Mai shari’a Ijeoma Ojukwu na babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta yi watsi da bukatar da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya mika mata inda yake kalubalantar shari’ar da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta ke yi masa.

Mai shari’ar ta bayyana cewa Sule Lamido yana da tuhumar da zai amsa a gaban kotu.

Ijeoma Ojukwu ta yanke wannan hukunci ne a jiya.

Sule Lamido yana fuskantar shari’a tare da ‘ya’yansa biyu: Aminu Sule Lamido, Mustapha Sule Lamido, da abokin kasuwancinsa, Aminu Wada Abubakar da kamfanoni hudu bisa laifuka 37 da aka gyara wadanda suka shafi karkatar da kudade har naira miliyan 712.

Mai shari’a Ojukwu ya amince da maganar da lauyan EFCC, Chile Okoroma, ya yi cewa Sule Lamido na da tuhumar da zai amsa sannan ta umarce shi da ya yi shirin kare kansa a ranar da za a dawo cigaba da sauraron shari’ar.

Mai shari’ar ta dage sauraron karar zuwa ranar 8 zuwa 11 ga watan Nuwamban bana domin tsohon gwamnan ya fara kare kan sa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen − twelve =