Kebbi: Za’a biya mafi karancin albashi na 30,000 daga watan Satumba

111
Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu

Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya amince da fara biyan mafi karanci albashi na naira 30,000 daga wannan watan na Satumba.

Sanarwan biyan mafi karancin albashin ya fito ne daga bakin sakataren gwamnatin jihar Babale Yauri inda yace za’a fara biyan kudin a wannan watan ba tare da bata lokaci ba.

A yanzu dai jihar Kebbi itace jihar farko a duk fadin Najeriya da ta amince da fara biyan mafi karancin albashin.

Tun a watan Afrilu na wannan shekarar ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan amincewa da biyan mafi karancin albashin, amma har yanzu babu wata jiha da ta aiwatar da hakan, in banda jihar Kebbi da a yau Litini ta bayyana cewa zata fara biyan kudin a wannan watan na Satumba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty − four =