Kauyaka 11 ne ambaliya ta mamaye a Ringim jihar Jigawa

182

Akalla kauyuka 11 ne ambaliyar ruwa ta mamaye a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.

Shugaban karamar hukumar, Shehu Sule Udi ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Ringim.

Ya ce ambaliyar ruwa ta yi barna tare da raba mutane da muhallansu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, tare da lalata daruruwan gidaje da filayen noma da sauran dukiyoyi sakamakon ambaliyar da madatsar ruwa ta Tiga ta yi.

Ya bayyana cewa ambaliyar ta tashi kauyukan Dabi, Majiyawa, Dingare, Gabarin, Yandutse, Malamawar, Cori, Gujaba, Sankara, Auramo, Garin Gada da sauransu.

Sule Udi ya ce karamar hukumar ta kwashe wadanda abin ya shafa tare da mayar da su sansanonin ‘yan gudun hijira a garuruwan Ringim da Gerawa.

Ya ce karamar hukumar ta kuma ba su abinci da ruwan sha mai kyau da magunguna. Shugaban karamar hukumar ya bukaci jihar da gwamnatocin tarayya da sauran daidaikun jama’a da su gaggauta kai dauki ga wadanda abin ya shafa.

A wani labarin mai alaka da wannan, hukumar raya kogunan Hadejia da Jama’are ta ta’allaka yawan ambaliyar ruwan da ake ga mamakon ruwan sama da ake samu, ba wai sakin ruwa daga madatsar ruwa ta Tiga ko Challawa Goje.

Manajan Daraktan Hukumar, Injiniya Ma’amun Da’u Aliyu ya bayyana haka ta cikin wani shirin Radio Jigawa.

Yace manoma da suke karya hanyoyin ruwa da zummar yin noman rani ya taimaka wajen samun ambaliyar ruwa a garuruwan dake gabar Kogin Hadejia da Jama’are.

Injiniya Ma’amun Dau ya gargadi manoma su guji yanka hanyoyin ruwa da zummar yin noman rani ba tare da samun shawarwarin kwararru ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seventeen − 6 =