Gwamnati ta bukaci jami’o’i su nemi tallafin masu hannu da shuni

64

Gwamnatin tarayya a jiya ta bukaci majalissar gudanarwar jami’o’i da su nemi goyon bayan kungiyoyi da kuma daidaikun mutane domin samun karin kudaden gudanar da ayyuka.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya bayar da wannan shawarar jiya a Abuja, yayin da yake kaddamar da majalisun gudanarwar jami’ar noma ta tarayya dake Abeokuta, jihar Ogun, da jami’ar noma ta Michael Okpara dake Umudike, Jihar Abia, da jami’ar noma ta Joseph Sarwuan Tarka dake Makurdi, Jihar Benue, da kuma jami’ar noma ta tarayya dake Zuru, Jihar Kebbi.

Adamu Adamu, wanda karamin ministan ilimi, Goodluck Opiah ya wakilta, ya bayar da misali da lokacin matsin tattalin arziki da kuma burin gwamnati na kawo karin kamfanoni masu zaman kansu a manyan makarantu, inda ya nemi majalisun gudanarwar da su bullo da dabarun da za su samar da karin kudaden shiga ba tare da kason gwamnati ba.

Ya kuma bukaci majalisun gudanarwar su taka rawar gani da nuna kwarewa da kuma samar da irin jagoranci da zai kara habaka ci gaban jami’o’in cikin sauri.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 − one =